2024-05-10 21:37
Wato jiya na je asibiti dubiya, sai wani dattijo ya rasu, a kan idona ya yi numfashinsa na ƙarshe.
Yadda na ga iyalinsa suna kuka da yadda aka naɗe shi, wallahi har yanzu na kasa samun nutsuwa. Na rasa me ke min daɗi a duniya.
Tabbas mutuwa aya ce!
Allah ina roƙonka lokacin da zan zo gare ka ya zamana kana alfahari da ni ba don ni ba don darajar Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad SAW.
ZUCIYATA ZAFI TA KE MIN WALLAHI!
😭😭😭😭😭😭😭